Cikin shekaru 2, sama da likitoci 9,000 sun bar Najeriya zuwa Ƙasashen Waje — Cewar NMA
Kungiyar Likitoci ta Nijeriya, NMA, ta ce kasar ta yi asarar sama da likitoci 9,000 ga kasashen yamma tsakanin 2016 zuwa 2018, wanda hakan ya nuna cewa ƙasar nan na fatarar likitoci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Cross River Ta Musanta Zargin Rashin Kin Biyan Albashin Ma’aikata A Jihar
Shugaban kungiyar ta NMA, Farfesa Innocent Ujah ne ya bayyana haka a taron lacca na shekara-shekara na kungiyar a Abuja a jiya Litinin.
Ujah ya nuna damuwa game da kalubalen fatarar likitoci a bangaren kiwon lafiya.
Shugaban na NMA ya bayyana rashin amincewa da karancin ma’aikata ganin yadda kasar ke kan matakin likita 1ganduk mutane 5,000.
Da yake korafin cewa hakan ya na yin illa ga tsarin kiwon lafiyar kasar, Farfesa Ujah, wanda kuma shi ne mataimakin sh5ugaban Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Otukpo, ya ce Afirka, ciki har da Najeriya, na fuskantar matsalar ma’aikatan lafiya.