• “Tun kafa Kaduna a mulkin Dimokuradiyya ba a ta ba yin Sanatan da ya gabatar da guduri 19 ba a zauren majalissa.” Inji Uba Sani
• “Cikin shekarun biyu nayi wa al’umar da nake wakilta aikin Naira Billiyan 5”. Inji Sanatan.
• “An kusan amincewar da fara ginin gwamnatin tarayya dake Rigasa” a cewar sa.
A wata bibiya da Jaridar Dimokuradiyya ta yi cikin wata fira da Gidan radion Freedom Kaduna ta sanya da bisalin karfe 8:30 na daren jiya, ta yi hira da Sanata Malam Uba Sani wakilin kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Naijeriya. Malam uba sani ya bayyana kadan daga Cikin irin kokari tare da aikin Alkharin daya kai wa Al’ummar da yake wakilta, tun bayan zuwansa majalisar tsawon Shekaru biyu.
inda Sanatan ya bugi kirji yana mai cewa, “A tarihin jihar Kaduna tun bayan kafuwarta a mulkin Dimokuradiyya, babu wani Senata da ya tabayin kudurori guda goma sha tara 19 sai ni Uba Sani” inji shi.
Sanatan yace “Wanda muke sa rai daya daga cikin kudurorin Shugaba Buhari zai sa masa hannu kan Kudirin asibitin tarayya (Federal Medical center Rigasa) bayan Majalisar wakilai sun gama mahawara, domin tuni majalisar dattijai suka riga suka gama nasu muhawarorin kan kudirin” a cewar sa.
Sanatan ya kara da cewa kawo yanzu, Na kawo ma mutanan Kaduna ta tsakiya, aiyuka na a kalla sama da Naira Bilyan biyar 5bn, a cikin shekaru biyu kacal kachal da nayi a majalissa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje zai biya Dalibai marasa galihu guda 10,000 kudin jarabawar NECO
“Kuma na sanya an gina makatantar kwana dake Kawo, cikin garin Kaduna, ICT center wanda aka zuba Na’ura Mai Kwakwalwa guda dari biyar, duk domin inganta karatun yaranmu.” Inji sanatan
Idan zaku iya tunawa dai, Sanata Uba Sani ya samu lambobin yabo kan wakilci na gari ga Al’ummarsa, musamman yadda sanatan ya shahara wajen samar da jari ga matasan Jihar Kaduna, dama wasu dake Arewacin Naijeriya.