Dattawan jihar Imo sun ja kunnen ‘yan adawa da su daina kiran gwamnan jihar da ‘Gwamnan Kotun Koli,’ inda suka ce yin hakan cin mutunci ne ga gwamna Hope Uzodinma.
Dattawan sun tabbatar da cewa amfani da irin wannan sunan wajen kiran gwamna ba kawai cin mutunci bane, a’a zagi ne ma ga al’ummar jihar Imo baki daya, wanda hakan ke nufin kamar ba al’ummar jihar bane suka zabe shi.
Har wala yau Dattawan sun ce suna goyon bayan binciken da majalisar jihar za ta yi kan zargin bacewar kudi naira biliyan 19.63 da ake zargin tsohon gwamnan jihar Emeka Ihedioha ya yi.
Bayanan na fitowa ne a sanarwar da Dr Edmond J K Onyebuchi, shugaban kungiyar Dattawan Jihar ya fitar.