Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba a ranar Litinin ya yi Allah-wadai da yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan jami’an ‘yan sanda da maza da ke sanye da kayan aiki, inda suke gudanar da ayyukansu na tabbatar da doka a sassa daban-daban na kasar nan, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
IGP a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya jaddada cewa hare-haren da ake kaiwa jami’an ‘yan sanda, ya sabawa doka da oda.
Ya kuma yi gargadin cewa, ba za a sake lamuntar kai wa jami’an hari ta kowace irin salo ba, yana mai bayyana cewa rundunar ta rike rayukan jami’anta da mutunci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Cigaba Da Gwabza Kazamin Fada Tsakanin Yan tawayen Tigray Da Dakarun Habasha
Don haka, shugaban ‘yan sandan ya umurci dukkan ‘yan sanda da tsare-tsare da su tabbatar da cewa sun kama mutanen da suka kai wa jami’an ‘yan sanda farmaki, ba tare da la’akari da abubuwan da ko suwaye ba, kuma a gurfanar da su domin su fuskanci fushin doka.
IGP yayin da yake nanata kudurin rundunar na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin kasar nan, ya jaddada mahimmancin mutunta hakkin dan Adam da ke cikin tsarin aikin jami’an ‘yan sanda.
DAILY POST ta ruwaito cewa faifan bidiyo na masu ababen hawa da wasu fararen hula da ke cin zarafin jami’an ‘yan sanda na ta yawo a shafukan sada zumunta.
A WANI LABARIN KUMA: “Yakamata A Wargaza Kungiyar ASUU, Ba Ta Da Amfani”—–Dan Gwamnan Jihar Kaduna
Bashir, daya daga cikin ‘ya’yan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Litinin, ya bayyana kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU a matsayin “kungiyar da ba ta da amfani”, inda ya cigaba da cewa ya kamata a wargazata a maye gurbinsu da malamai masu kula da damuwar dalibai.
Punch ta ruwaito cewa, Hakan na zuwa ne bayan ASUU ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take yi.