Chelsea ta cimma matsaya kan yarjejeniyar sirri da dan wasan bayan Leicester City Wesley Fofana, in ji Ignazio Genuardi.
Ana tunanin Chelsea na neman wani dan gwararran dan wasan baya bayan ta rasa siyan Jules Kounde, wanda ke shirin komawa Barcelona daga Sevilla a cikin kwanaki kadan masu zuwa.
Fofana dai ana alakanta shi da barin Leicester a kakar wasa ta bana kuma da alama yanzu Chelsea ta dauki matakin kawo shi Stamford Bridge.
Har yanzu Chelsea ba ta cimma matsaya kan farashin dan wasan ba tsakaninta da kungiyar Leicester, duk da haka, akwai yiwuwar Leicester City za ta bukaci kudi mai yawa domin ta bar Fofana kafin a fara sabon kakar wasa a watan Agusta mai kamawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Ta Amince Da Karin Kashi 50 Na Tallafin Karatu Ga Daliban Jihar
A wani labarin kuma na daban.
Surukina Tinubu Shekarun Shi 86, Bai Cancanci Zama Shugaban Kasa Ba – Tee Mac
Shahararren mai kada sarewa, Tee Mac Omatshola Iseli ya bayyana dalilan da ya sa dan takarar shugaban kasa karkashin jnuwar jam’iyar APC, Bola Tinubu, bai kamata ya zama shugaban Najeriya ba.
Tee Mac yayi ikirarin cewa Tinubu yana da shekaru 86 don haka kuma bai cancanci zama shugaban Najeriya ba.
Tsohon shugaban kungiyar mawaka ta Najeriya, PMAN, ya ce shi da matar Tinubu, Remi ’yan uwa ne amma ya daina goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2015 saboda ya nemi ‘yan Najeriya su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da yake mayar da martani ga wani ma’abocin Facebook, Yemi Olakitan, wanda ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, Tee Mac ya ce ya daina ziyartar gidan Tinubu da goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC duk da kasancewarsa suruki.
Ya wallafa cewa: “Ya kai Yemi, kowa zai iya zaɓar kowane ɗan takara amma mai hankali zai yi wa kansa tambayar: shin na zaɓa wanda ya dace! Shin mutumin ya cancanta? Shin mai gaskiya ne? Shin yana gaya mana gaskiya game da shekarunsa, tarihinsa, da kuma yadda ya sami kuɗinsa? Shin mutumin yana da koshin lafiya yana da shekaru 86, zaj iya ɗaukar aikin ƙasar da ta lalace gaba ɗaya?
“Ka ga, Tinubu surikina ne. Matarsa Remi ƙanwata ce, mahaifiyarta Itsekiri da mahaifiyata Itsekiri yan uwan juna ne. Na san Tinubu tun tsakiyar shekarun 80s da kaina har ma na shirya shi ya zauna a gidan ubana (SIR MOBOLAJI BANK-ANTHONY) a Landan lokacin da ya tafi gudun hijira.
“Na daina ba shi goyon baya, na daina ziyartar dangisa da sauransu lokacin da ya tallata wa al’umma shugaba Buhari a shekarar 2015.
“Don haka Ina shawartar al’umma cewa wannan mutumi bai cancanci zama shugaban mu ba” inji shi