Cire tallafin mai: TUC ta gaya wa Gwamnatin Tarayya abin da Ƴan Najeriya ke so kawai
Festus Osifo, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ba sa kyamar cire tallafin mai na kowacce lita (PMS) amma suna jiran Gwamnatin Tarayya ta samu amincewar su kan lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: COEASU Ta ce Tana Gab da sake Garƙame Kwalejojin Ilmi, ta tafi Yajin Aiki
Osifo ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Najeriya (NAEC) a Legas ranar Alhamis.
A cewarsa, yawancin ƴan Najeriya ba su da sha’awar canjin makamashi wajen al’amuran su na yau da kullum, amma sun damu ne kawai game da makamashi mai arha da zasu rayu dashi.
Osifo ya ce, “Ya kamata fadar shugaban kasa ta fito ta ce tana rage kasafin kudin su. Majalisar dokokin kasar ma na bukatar yin hakan. Wannan yana jagorantar misali.
“Yan Najeriya ba sa son cire tallafin, amma dole ne gwamnati ta kasance a shirye don nuna cewa zata iya cire tallafin ba dole sai da magana ba.
“Dole ne gwamnati ta nuna cewa idan tallafin dole ne ya tafi, dole ne wannan ya nuna a cikin iliminmu, dole ne ya nuna a fannin kiwon lafiyarmu da kuma matakan samar da ababen more rayuwa.
“Don haka dole ne a magance tabarbarewa da ‘yan Najeriya suka yi kafin mu samu ci gaba.
A wani labarin kuma: Rashin Tsaro ya sanya har yanzu ba a bude Makarantu Sakandare 75 a Zamfara – Ma’aikata
Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da ba’a bude Makarantun Sakandire 75 a Jihar Sakamakon rashin tsaro.
Babban Sakataren Ma’aikatar Alhaji Kabiru Attahi ne ya bayyana hakan a yayin wani taro na yini biyu na Matakin Jiha don tattauna manufofin kasa kan ilmin jinsi (NPGE) a Jihar.