Ƙungiyar Ƙwadago ta Kasa reshen Jahar Kano ta bayyana matakin da Gwamnati ta ɗauka na sake yin dubi akan tallafin man fetur, tare da ƙara kuɗin litar man fetur matsayin abun nasara ga ƴan Najeriya.
Dayake jawabi ga Manema Labaru a Kano, Shugaban Ƙungiyar Kabiru Ado Minjibir ya bayyana matakin a matsayin abun fata ga ƴan Najeriya da Al’umma gaba ɗaya.
KARANTA WANNAN LABARIN: An gurfanar da wani Dilan Mota sakamakon cin Naman Ƙaramin yaro a Zamfara
Jaridar Daily Truta ruwaito cewar Ƙungiyar Ƙwadago data ƴan kasuwa sun bayyana kudirin su na shiga yajin aiki akan gwamnatin tarayya.
Ƙungiyoyin sun bayyana ƙudirin su na yin fatali da cire tallafin man fetur ɗin.