Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kusan sabbin masu kamuwa da cutar kansa miliyan 1.1 na faruwa kowace shekara a Afirka, inda kusan 700,000 ke mutuwa.
Daraktar WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ta bayyana hakan a ranar Lahadi a cikin sanarwarta na bikin ranar cutar daji ta duniya na bana mai taken ‘Rufe Tazarar Kulawa: Haɗa Muryoyinmu da Daukar Mataki’.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kudu Zai Rantsar Da Sabbin Alkalai Takwas
Ta ce hasashen da aka yi a halin yanzu ya nuna cewa, Afirka za ta kai kusan kashi 50 cikin 100 na cutar kansar yara a duniya nan da shekarar 2050.
Moeti ta ce tare da gagarumin kalubalen bayanai, an kiyasta kamuwa da cutar kansar yara a yankin kudu da hamadar Sahara da kashi 56.3 a cikin kowace al’umma.
A cewarta, alkalumman bayanai sun nuna karuwar mace-macen cutar daji zuwa kusan mutuwar mutane miliyan daya a kowace shekara nan da shekara ta 2030, ba tare da daukar matakan gaggawa ba.
Ta ce: “Ya kamata mu tuna cewa ciwon daji da aka fi sani a manya sun hada da nono wanda ya dauki kashi 16.5%, sai kansar mahaifa kashi 13.1%, sannan prostate kashi 9.4%, Colorectal kashi 6%, da kuma hanta mai kashi 4.6%, yana ba da gudummawar kusan rabin sabbin masu kamuwa da cututtukan daji.”
Moeti ta ce kasashe 12 na yankin suna da ingantattun tsare-tsare na hana cutar daji ta kasa.
Ta ce hukumar ta WHO tana tallafawa karin kasashe 11 wajen bunkasa ko sabunta tsare-tsare na yaki da cutar daji na kasa wadanda suka yi daidai da shirye-shiryen cutar kansa na duniya tare da kasancewar tsarin mulki a matakin gwamnati don aiwatar da tsare-tsaren cutar kansa.
Ta ce abin farin ciki ne ganin yadda ake ci gaba da samun karuwar allurar rigakafin cutar ta Human Papilloma Virus (HPV) da kashi 51 cikin 100 na kasashen yankin, duk da cewa ya kai kashi 21 cikin dari.
Moeti ta ce, duk da wadannan nasarorin da aka samu, abubuwan da ke kawo cikas sun ci gaba da kasancewa a kan hanyar nahiyar, ciki har da karancin samar da rajistar masu cutar kansa, da karancin inganta kiwon lafiya, da rashin isassun hanyoyin rigakafin farko da ayyukan ganowa da wuri, da karancin wuraren bincike da ke kara samun jinkiri wajen gano cutar da jiyya da sauransu.
Ta yi kira ga gwamnatoci da su samar da / sabunta tsare-tsaren kula da cutar kansa na kasa, samar da kudade mai dorewa da kuma saka hannun jari a rajistar cutar kansa.
A wani labarin kuma, Tabarbarewar Kudi: Emefiele Yana Yakar Rashin Samun Nasarar Takararsa Ta Shugaban Kasa Ne – Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi zargin cewa da gangan ne gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya aiwatar da manufar musanya kudin Naira a matsayin dabarar yaki da rashin samun tikitin tsayawa takararsa ta shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wani gangamin yakin neman zabe da aka gudanar a Tsanyawa a ranar Lahadi, inda ya gabatar da ‘yan takarar gwamna da mataimakin gwamna na jam’iyyar tare da sauran ‘yan takara ga masu kada kuri’a.