Ministar Jin Kai ta Nijeriya Sa’adiya Umar Farouk ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe naira miliyan N523.3 domin ciyar da yara a lokacin kullen Coronavirus da aka yi a Nijeriya.
Ministar ta fadi hakan ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan cuwar coronavirus da aka gudanar yau Litinin a birnin tarayya Abuja.
Ta ce kudaden an kashe su ne a jihohi uku da gwamnatin tarayya ta kulli saboda coronavirus, a inda kowane gida aka kashe masa N4,200 duk wata.
Ta ce sun yi amfani da kididdigar NBS da CBN inda suka ce kowane gida akalla za a iya samun kananan yara guda uku a ciki, a inda aka kashe ma yaro daya abincin naira N70 sau talatin zai kama yaro zai lashe 1400, idan ka hada na yara uku a cikin gida daya ya kama naira N4200 kenan a wata.
Jihohin da aka ciyar da yaran sun hada da jihar Lagos da Ogun da kuma birnin tarayya Abuja.
Jimillar gidajen da aka ciyar a wadannan jihohin 124,589 idan ka yi sau 4200 zai baka N523,273,800
Ta Kuma bayyyana cewa sun gayyato hukumomin gwamnati irinsu EFCC da CCB, da ICPC, da DSS da kuma sauran kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba domin su shedi yadda ake raba abincin.
Sai dai al’ummah daban-daban sun mayar mata da martani kan hakan, inda aka bayyana zancen da Sunan karyane, kana kuma wasu gamayyar al’umma suka nemi shugaba Buhari ya sauka daga karagar mulkinsa in bazai iya ba da ya dinga yi ma mutane karya.