Cocin Katolika ta dawo Musabahar hannu, bayaj wucewar COVID-19
Cocin Katolika ta ba da sanarwar dawo da musafaha na gargajiya a cikin majami’u, wanda aka dakatar yayin bala’in COVID-19.
Rev. Lucius Iwejur-Ugorji, Archbishop na cocin diocese na Owerri ya bayyana haka a cikin wata sanarwa cewa masu ibada za su dawo da “Musabahar sada zaman lafiya” a lokacin Eucharistic da sauran abubuwan da suka faru a cikin bukukuwan liturgical na Cocin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu Kashe Naira Billiyan 1.2 Domin Gyaran Wasu Hanyoyi—Gwamnatin Kano
Sanarwar ta samu sa hannun Rabaran Fr. Cosmas Uzoigwe, Mataimakin Shugaban Cocin, kuma ya saki ta hannun Daraktan Sadarwa na Jama’a na cocin, Fr Mike Umoh, ranar Lahadi a Abuja.
Sanarwar ta yi jawabi ne ga daukacin limaman coci da kuma ‘yan’uwa da ke Owerri Archdiocese.
“Za a iya tunawa cewa cutar ta COVID-19 ta tilasta mu mu furta tsattsauran ka’idoji wadanda suka shafi ibadarmu, kuma daya daga cikin irin wadannan shi ne wanda ya hana kowa daga musabaha yayin taro
“Kudirin fara gudanar da musabaha na musabaha ya zo ne biyo bayan kammala taron bishop na Katolika na Najeriya da aka kammala kwanan nan a Orlu.
“Mun gode wa Allah da ya jagorance mu a lokutan kalubale na annobar COVID-19, muna addu’a gare shi da ya albarkace mu a koda yaushe tare da kasancewar sa,” in ji Archbishop. (NAN)
A wani labarin kuma: Yan Majalissar Wakilai Zasu Koma Zama, A Wani Wuri Na Daban
Majalisar wakilai za ta dawo zamanta a ranar 20 ga Satumba, a zauren wucin gadi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da magatakardar majalisar, Yahaya Danzaria, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.