Kungiyar Malaman kwalejojin ilimi na Nijeriya wato COEASU, sun yi ma gwamnatin tarayya barazana fadawa yajin aiki na dindindin matukar ba ta amince da bukatunsu ba.
Kungiyar ta yi wannan barazana ne sakamakon yin watsi da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da gwamnatin tarayya game da wasu muhimman bukatunta da ta mika ma gwamnati gabanin janyewar wancan yajin aiki da ta yi.
Shugaban kungiyar, Nuhu Ogirima tare da Sakataren kungiyar, Taiwo Olayanju ne suka rattaba hannu a kan sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Talata, 17 ga watan Satumba bayan kammala taron kungiyar da aka daga ranar 10 zuwa 11 ga wata a Legas.