COEASU Ta ce Tana Gab da sake Garƙame Kwalejojin Ilmi, ta tafi Yajin Aiki
Kungiyar malaman kwalejojin ilimi (COEASU) ta yi barazanar komawa yajin aikin mako biyu da ta dakatar idan har Gwamnatin Tarayya ta gaza maida albashin ma’aikata data cire.
Kungiyar ta ce rashin da’a ne, da rashin bin ka’ida, kuma babban laifi ne a riƙa cire musu albashi ba tare da mika su ga hukumar da ta dace ta hanyar Integrated Payroll and Personnel Information System (IPPIS).
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ku Sanya Nijeriya A Gaba – Jonathan Ga Ƴan Siyasa
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ta COEASU na Ƙasa, Olusegun Lana ne ya yi wannan gargadin ranar Alhamis yayin da yake zantawa da Manema Labarai a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Kungiyar ta COEASU ta dakatar da yajin aikin da ta shafe watanni biyu tana yi na tsawon kwanaki 60 domin baiwa gwamnatin tarayya damar aiwatar da wasu batutuwan da ƴan Ƙungiyar suka amince da su.
Lana ya ce kungiyar ta kasa ta je Ogun ne domin warware rikicin da ya barke tsakanin malaman kwalejin ilimi ta Tai Solarin (TASCE) da gwamnatin jihar.
Ya ce “Muna gargadin gwamnatin tarayya da ta gaggauta yin wani abu game da kalubalen da IPPIS ya janyo. Kasancewar majalisar zartaswa ta kasa ta dakatar da yajin aikin ba ya nufin har yanzu ba za’a iya dawowa domin har yanzu IPPIS na zama babban kalubale ga tsarinmu.
“Yayin da muke magana, har yanzu IPPIS ta hana cirar da wasu daga cikin albashin mu a kwalejojin tarayya. Wannan bai gamsar ba, idan kun biya ne albashi, me ya sa kuke hana cirewa na ɓangare na uku?
“Muna gargadin gwamnatin tarayya da ofishin Akanta Janar na tarayya da su yi wani abu cikin gaggawa kan wannan batu ba tare da bata lokaci ba domin hakan na iya yin barazana ga zaman lafiyar da muka kulla da gwamnatin tarayya.”
A wani labarin kuma:2023: Ku Sanya Nijeriya A Gaba – Jonathan Ga Ƴan Siyasa
Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bukaci ƴan siyasa da su riƙa lura da haɗin kai da walwalar ƴan Najeriya a yakin neman zaben su da sauran ayyukan zaɓen 2023 mai zuwa.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Abuja Yayin taron Shekara-shekara na tunawa da ayyukan alheri na Tsohon Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida