Shugaban kungiyar kwallon kafa ta West Ham, Karren Brady ya ce har yanzu babu takamaimen ranar dawo wa a ci gaba da buga wasannin gasar Firimiyar Ingila. Duk da cewa an sanya watan Yuni a matsayin watan da za a dawo a ci gaba da gasar.
Sai dai sakamakon yadda cutar Korona ke ci gaba da yiwa kasar ta Birtaniya barazana da sake yaduwa da kisa a tsakanin al’ummar kasar, a halin yanzu babu takamaimen ranar da za a dawo a ci gaba da gasar.
Hukumumin masu shirya gasar Firimiyar sun ce suna fatan sun karasa sauran wasanni 92 da suka rage, amma ci gaba da bayyanar Korona babu takamaimen lokacin dawo wa.