Kungiyar MOSOP ta bayyana kaduwarta da damuwarta bisa mutuwar da ga Marigayi Ken Saro-Wiwa, wato Menegian Saro-Wiwa sakamakon cutar Coronavirus da ta kama shi a Birtaniya.
Hakan na fitowa ne daka cikin wata sanarwa da Chief Keeper Gbaranor, shugaban kungiyar ta MOSOP ya sanya hannu a garin Fatakwal a ranar Juma’a.
Shi dai Marigayin Menegian, an haife shi ne a shekarar 1970, kuma shi da na karshe da yake rayuwa ga Saro Wiwa.
MOSOP sunce sun samu labarin mutuwarsa ne ta hanyar sakon Imel da suka samu daga Birtaniya daga ‘yaruwarsa Noo Saro-Wiwa, wanda ta tabbatar da rasuwarsa a ranar Alhamis.