Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya takaita zirga-zirga a jihar baki daya, inda ya ayyana dokar takaita zirga-zirga daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yammaci a kowacce rana.
Wannan dokar da ya bada umurni ita ce ta farko da ya bayar tun bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar.
Uzodinma, ya
ayyana dokar ne a dare jiya Juma’a domin ganin an dakile yaduwar cutar Korona a
jihar, duk da har ya zuwa yanzu ba a tabbatar da mai Korona din a jihar ta Imo
ba.
Ya zuwa yanzu dai,
NCDC sun ce mutum 493 ne suke da cutar a Nijeriya, a yayin da mutum 17 suka
mutu ciki harda Abba Kyari a yayin da mutum 159 suka warke daga cutar.