By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Gombe ta ce tana saran yiwa mazauna jihar miliyan 1.9 allurar rigakafin cutar COVID-19 kafin karshen watan Maris.
Manajan aikin na Cibiyar Kula da rigakafin Gaggawa ta Jiha (SERICC), Musa Ibrahim Kuna, ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar don bunkasa rigakafin allurar cutar COVID-19 a jihar.
Kuna ya ce mutane 15,945 ne kawai aka yi wa allurar rigakafin cutar.
Ya bayyana cewa adadin wadanda aka yiwa allurar a jihar ya nuna kashi 12 cikin 100 na alluran farko da kashi shida cikin dari a zango na biyu.
A nasa bangaren, mataimakin gwamnan jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya ce an kira taron ne domin tattara bayanai daga mahalarta taron kan yadda za a inganta darajar allurar.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na Jihar, Julius Ishaya Lepes, ya bada shawarar wayar da kan jama’a da su taimaka wajen sauya labari ta hanyar sanar da jama’a muhimmancin rigakafin tare da tabbatar wa ‘yan kasar cewa allurar ba ta da illa.