Gwamnatin Tarayya ta lissafa wasu ƙa’idoji ga masu shigowa Najeriya, bayan Ƙasar Landan ta dakatar da dokokin data sanya ga wanda aka yiwa rigakafin Covid-19 daga Nigeria.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin Shugaban ƙasa akan cutar Covid-19 Boss Mustapha, ya bayyana cewa, dukkanin waɗanda zasu shigo Nigeria da aka yiwa rigakafi, sai sun bayyana takardar dake nuna cewa basa ɗauke da cutar, a yayinda waɗanda basu yi rigakafin ba, to zasu killace kansu.
“Waɗanda ba’a yiwa rigakafi ba duka, to zasu killace kansu na tsawon kwanaki 7, ƙari bisa ga gwajin cutar da za’ayi masu a cikin kwanaki biyu da 7 bayan sun iso.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Dokar Ta Baci A Manyan Hanyoyin Kasar
“Waɗanda aka yiwa rigakafin duka, bazai killace kanshi ba na tsawon kwanaki 7, amma za’a buƙaci yayi rigakafi a kwana biyu bayan ya iso Nigeria.
Sanarwar ta kuma bada wasu ƙa’idoji ga matafiya zuwa Nigeria na wani ɗan lokaci, inda yace dole sai anyi masu rigakafi kafin a barsu su shiga ƙasar.
“Mutanen dake zuwa Nigeria domin kasuwanci ko wani aiki na musamman, dazai zauna ƙasa da kwanaki 7, dole sai anyi mashi rigakafi duka, tare da gabatar da takardar dacewa baya ɗauke da cutar, inji sanarwar.
Idan dai za’a tuna Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa akan cutar Covid-19 Boss Mustapha a lokacin da yake jawabi, yasha alwashin buga dukkanin dokokin da aka sake dubi akansu.