Ƙasar Landan ta hana ƙasar Afirka ta Kudu da wasu ƙasashe maƙwabtan ta shigowa ƙasar, akan yiwuwar samun wata samfarin cutar Covid-19 da aka gano a kwanakin baya a yankin.
Acewar Bloomberg, Hana shiga ƙasar zai fara ne a ranar Juma’a da safe, wanda anyi haka domin hana yaɗuwar sabuwar samfarin cutar da ake bincike akan ta, kamar yadda Sakatare Sajid Javid ya bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: An Sace Shugaban Makaranta, Mataimakinsa, Da Wasu Malaman A Jihar Ondo
Ƙasashen guda 6 Landan zata sanya su akan jadawalin da zata riƙa sanyawa suna kulle kansu a otel ɗin ƙasar.
Ƙasar Singapore a ranar Juma’a tayi yunƙurin hana ƙasar Afrika ta Kudu da sauran maƙwabtan ta zuwa ƙasar.
Masana kimiyya har yanzu suna ta ƙoƙarin gano cewa ko sabuwar samfarin cutar da ake kira B.1.1529 tafi saurin yaɗuwa akan wadda aka gano.
Firmanistan Ƙasar Landan Boris Johnson yace hana zirga-zirgar shigowa ƙasar ya shafi ta sama ne, wanda an ɗauke shi ne domin hana shigowa da sabuwar samfarin cutar zuwa ƙasar.