Cibiyar Kula da Cutuka ta Kasa, (NCDC) ta ce Najeriya ta tabbatar da sama da mutane 250,000 da suka kamu da cutar coronavirus tare da samun mutuwar sama da 3,000 a cikin shekaru biyu da suka gabata.
A wata sanarwa da hukumar NCDC ta fitar, ta ce Najeriya ta koyi manyan darussa a yunkurinta na karfafa tsarin kiwon lafiyarta domin tinkarar wasu cututtuka masu yaduwa da kuma matsalolin gaggawa na lafiya a nan gaba.
“Wannan ya sa yana da mahimmanci ace an koyi wasu darussan da wannan annoba ta koyar don ƙarfafa shiri da mayar da tunkarar wasu cutukan daidai da irin umarnin da Muka bayar. Mun ci gaba da fuskantar barkewar cutar kwalara da zazzabin Lassa a lokaci guda tare da cutar ta COVID-19”.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Ranar 27 ga watan Fabrairu ne dai aka cika shekaru biyu da samun bullar cutar Coronavirus ta farko a Najeriya.
Hukumar NCDC ta ce har yanzu coronavirus na ci gaba da kasancewa gaskiya a duniya tare da haɗarin bullar bambance-bambance masu haɗari duk da yawan gajiyawar cutar.
Cibiyar ta ce tana ci gaba da daukan darussa kan yadda ake tunkarar cutar a cikin shekaru biyu da suka gabata domin karfafa harkokin kiwon lafiya a kasar.
“Dukkanmu muna da alhakin karfafawa da kuma ci gaba da daukar nauyin hukumomi don dorewar sha’awa da saka hannun jari a fannin kiwon lafiya gabaɗaya musamman don tsaron lafiya,” in ji shi.