Gwamnatin jihar Sakkwato ta rage kasafin kudinta na 2020 daga naira biliyan 202 zuwa naira biliyan 153 domin ganin an yafewa ‘yan jihar kudin ruwa har na tsawon wata biyu domi saukakawa al’umma sakamakon annobar cutar Coronavirus.
Kwamishinan kudi na jihar, Alhaji Abdussamad Dasuki, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Juma’a, inda ya ce an cimma wannan matsayar ne a yayin zaman da majalisar zartaswa ta jihar ta yi.
A cewarsa, waiwaye kan kasafin kudin ya zama wajibi ne duba da yadda kudi suka yi kasa sakamakon bullar cutar Corona, wanda ta durkusar da tattalin arzikin duniya.