A ci gaba da hadin guiwa wajen ganin an kawo karshen cutar sarke numfashi a Kano gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sake kaddamar da wasu sabbin cibiyoyin gwaji har guda biyu akan titin Independence road dake unguwar Bompai a ranar Alhamis.
Kungiyar E-Health Africa ta samar da cibiyar gwaji wanda zata iya daukar samfuri har guda 300 a rana. Ita kuwa Gidauniyar dakile cututtuka masu yaduwa ta samar da cibiyar gwaji wanda zata iya daukar samfuri 90 a rana.
A ci gaba da yaki da cutar gwamna Ganduje ya ci gaba da neman hadin guiwa da kungiyoyi masu zaman kansu da ma dai-daikun mutane.
Ya kara da cewa cutar ta yadu a wasu sassan jihar, dan haka gwamnatin nasa ta canja fasalin yaki da ita, gwamnatin zata shiga lungu da sako domin yakar cutar.
https://dimokuradiyya.com.ng/dangote-ya-gina-katafariyar-cibiyar-gwajin-korona-a-kano/
Gwamnan yana fatan cibiyoyin zasu ke daukar samfurin gwaji a kalla guda 300 a rana domin ganin an dakile cutar cikin kankanin lokaci tare da fatan samun karancin masu dauke da cutar.
Gwamnan ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da hadin guiwa da kungiyoyin domin yakar cutattukan da suka shafi harkar lafiya ba iya cutar Korona ba.
Daga bangaren wakilan kungiyoyin, Mataimakin Shugaban gudanarwa na kungiyar E-Health Africa Mista Atif Fawaz da kuma Mista Barnand Ebruka daga Gidauniyar dakile cututtuka masu yaduwa, sun bayyana cewa zasu ci gaba bawa gwamnati hadin kai wajen yaki da wannan anmoba.