Gwamnatin Kano ta yi feshin magani a Coci 31 a cikin birnin jihar domin dakile yaduwar cutar Corona kamar yadda Gwamna Ganduje ya bayyana.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da reshen kungiyar mabiya addinin kirista ta kasa (CAN) a gidan gwamnati.
Ganduje ya ce, ganawa da shugabannin mabiya addinin kirista ya zama dole domin kawo karshen wannan annoba.
Gwamnan ya roki shuwagabannin da sauran al’umma dasu bawa gwamnati hadin kai wajen ganin an dakile COVID19 a jihar ta Kano, kuma gwamnan ya yi alkawari kafa cibiyar gwaji a rukunin gidaje dake Sabon gari.
Ganduje ya yabawa shugabancin kungiyar mabiya addinin kirista (CAN) reshen jihar Kano bisa irin kokarin da suke na bin doka da bada tazara a wuraren bauta.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Rev. Samuel Adeyemo, ya yiwa Gwamna Ganduje godiya tare da yaba masa bisa yiwa Coci 31 feshin magani.
Adeyemo ya ce, suna godiya kwarai duba da yadda gwamnan ya bawa mabiya addinin nasu dama wajen fitowa ranar Lahadi domin gudanar da ibadarsu.
A wani cigaban kuwa, Ganduje ya bude cibiyar gwaji a masarautar Rano. Har wa yau, ya sake bude wata cibiyar a asibitin Waziri dake unguwar Bachirawa wanda Kungiyar eHealth ta bawa gwamnatin Kano gudunmawa.
Daga: Abubakar Muhammad Usman