Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Ghebereyesus, ya yi ikrarin cewa an siyasantar da batun annobar cutar Korona, wanda ya kira hakan da babbar barazana fiye da ita cutar.
A jiya Litinin ne Daraktan hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebereyesus, ya bayyana a wani taron gwamnatoci na kasa da kasa da aka yi ta kafar talbijin a Dubai inda, ya ce, “duniya tana matukar bukatar hadin kan kasashe da kuma goyon baya. Siyasantar da annobar ya wuce gona da iri.”
Tedros ya jaddada cewa babbar barazanar da ake fuskanta yanzu ba wai kwayar cutar ba ce illa rashin jagoranci nagari a fadin duniya.
Sai dai shugaban hukumar ta WHO bai bayyana hakikanin abinda yake nufi siyasantar da annobar ba.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya soki lamirin ita hukumar lafiya ta duniya game da yadda take yakar cutar ta Korona a fadin duniya, amma wasu masana siyasar duniya suna ganin wannan batu na Trump ba komai bane face kawo siyasa cikin lamarin.