Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya killace kansa biyon bayan gwajin da aka yiwa iyalai da makusantan kwamishinansa da ya rasu Solomon Ogunji, gwajin dai ya nuna makusantan nasa na dauke da wannan cuta ta sarke numfashi. Gwamnan ya bawa dukkanin masu ruwa da tsaki na gwamnatin da suka san sun yi hulda da mamacin da su killace kansu tare da yin gwajin cutar COVID19.
Hakan ya fito daga bakin kwamishinan yada labarai na jihar ne Cif John Kalu, wanda yace gwamnan har yanzu na ci gaba da jimamin rasuwar kwamishinan nasa, sai dai kuma ya umarci mataimakinsa da kuma duk wasu masu ruwa da tsaki da su yi gwajin cutar, kuma su killace kansu kafin fitowar sakamakon.