Gwamna Samuel Ortom ya bada umarnin bude Coci, Masallatai da sauran wuraren ibada.
Gwamnan ya sanar da soke dokar kulle akan wadannan wurare ne a yayin da yake tattaunawa da kwamitin kar ta kwana kan annobar sarke numfashi na jihar a Makurdi a yau Asabar.
Ortom yace gwamnatin nasa ta sake duba dokar ne bayan da gwamnatin tarayya tace yanzu yaki da cutar COVID19 ya dawo hannun gwamnatocin Jihar, shi yasa suka yanke hukuncin sake bude wuraren ibada.
Ya kara da cewa tunda jiha ce karkashin ikon gwamnatin tarayya dole ne su bi doka shi yasa a baya basu yunkurin hakan ba.
Kafin yanke hukuncin gwamnan sai da ya samu damar ganawa da shugabannin kungiyoyin addanin wanda suka hada da kungiyar mabiya addinin kirista da kuma kungiyar Jamatu Nasiru Islam.
Ortom ya bayyana cewa an sallami Mrs Elizabeth Apedzan, wadda ta kamu da cutar ta COVID19.
Ya kara kira ga jama’ar jihar cewa duk wanda yaji wani yanayi wanda yayi kama da na cutar to su garzaya domin yin gwaji.