A cikin wani faifan Bidiyo da ya zaga an ga malammin yana sukar gwamnatocin Najeriya, inda yace musulmi su kauracewa dokar da aka kafa tare da gudanar da Sallar Idi.
Sheikh Bello Yabo, wanda yake mazaunin jihar Sokoto ya soki gwamnati musamman gwamnatin jihar Kaduna inda yace ba komai bane face rashin kishin addinin musulunci.
https://dimokuradiyya.com.ng/muna-goyon-bayan-hana-sallar-idi-a-kaduna-wasu-malaman-jihar/
Malamin ya bayyana cewa Gwamna El-Rufa’i da ma wasu sauran gwamnoni da suka hana tarukan addini da Sallar Idi sam basu da kishin addinin musulunci, kuma malamin ya karyata annobar sarke numfashi inda yace ba gaskiya bace.
Malamin ya kara da cewa idan aka yi duba da kyau za a ga cewa addinin Allah ne ba a so a yi, saboda ana tunanin zuwa masallaci zai iya yada cutar COVID19 amma zuwa kasuwa da sauran wurare ba ya yada ta.