Gwamnatin Kano ta ce zata rage kasafin kudin bana da kaso 30 cikin 100, biyo bayan koma baya da annobar sarke numfashi ta haddasa.
Ganduje ya bayyana haka ne, a yayin da yake tattaunawa da manema labarai a dakin taro na ‘Africa house’ dake fadar gwamnatin Kano.
Gwamnan yace za a tura kasafin zuwa ga majalisar dokokin jihar domin sake yin duba da kuma sahalewa, duba da irin kalubale da aka cintsi kai a ciki.
Har wayau, gwamna Ganduje ya jinjinawa ‘yan jarida a jihar yadda suke kokarin wayar da kan al’umma game da cutar sarke numfashi.
Ganduje ya kara da cewa, gwamnatin nasa zata bude cibiyoyin lafiya a kowane sabbin masarautun da aka kirkira, dauke da sabbin kayan aiki domin a sama musu sauki.