Gwamnatin tarayya ta koka bisa karin samun mace-macen masu dauke da cutar Corona Virus, wanda ta ce hakan yana da alaka da yadda mutane suke daukan matakan kariya da kansu ba tare da neman shawarar masana ba, wasu kuma sukan zauna a gida ba tare da zuwa asibiti ba.
Boss Mustapha, wanda shi ne shugaban kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan cutar COVID19, ya ce yana da kyau duk wanda yake dauke da cutar ya nemi taimakon masana ba wai ya zauna a gida ba.
“Duk wanda yasan yana da dauke da cutar yana da matukar muhimmanci da yasan cewa kofofin taimako a bude suke a ko da yaushe, ba wai mutum ya zauna da cuta na damunsa ba, saboda ta hakan ne kawai za a iya ceto rayuwar mutane”.
Daga bangarensa Ministan Lafiya na kasa, Dakta Osagie Ehanire, ya kara da cewa mutane da dama sun gwammace nemawa kansu mafita akan su nemi taimakon masana.
Ya kara da cewa, labari mafi dadi shi ne ya zuwa yanzu an sallami mutane 1, 644, sai kuma mutane 191 da suka rasu wanda idan aka yi duba za a ga basu da yawa duba da wasu kasashen da zaka ga mutane da yawa sun rasa rayukansu. Ministan ya kara da cewa mafiya yawan mutanen da suke gudun taimakon Likitoci da masu mutane ne masu ilimi, sai daga karshe abubuwa sun cakude musu sannan zasu garzayo zuwa asibiti domin neman taimakon gaggauwa wanda hakan ba daidai bane.
“Bayanai sun bayyana cewa sarkewar numfashi yana farawa ne a hankali, shi yasa yake da kyau duk wanda aka tabbatar yana dauke da cutar yake neman shawarar masana”.
Daga: Abubakar Muhammad Usman