Gwamnatin tarayya ta ja hankalin ‘yan kasuwa da masu harkar sufuri da kada suyi karin kudi ga harkar kasuwancinsu duba da halin da kasa ke ci na yaki da annobar sarke numfashi.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan a yayin da yake tattaunawa da kwamitin kar ta kwana kan annobar ta sarke numfashi a ranar Alhamis a babban birnin tarayya, Abuja.
Ya ce ya kamata duk wani dan kasuwa ya fahimci halin da ake ciki a kasar nan, kuma ya bada gudunmawa wajen kin kara farashin kayan abinci da sauransu.
Ministan ya kara da cewa, wannan yanayin da ake ciki zai fi kyau idan aka taimaki al’umma maimakon a yi amfani da yanayin wajen cutar da su.
https://dimokuradiyya.com.ng/covid19-likitoci-8-sun-kamu-da-cutar-covid19-a-jihar-zamfara/
Lai ya sake yin kira ga Kungiyar masu sufuri (NUTRW) ta kasa da cewa kudin sufurin kayan abinci daga wani bangare na kasar nan zuwa wani bai kamata ya tashi ba.
Ya kara da cewa har yanzu wasu’ya’yan kungiyar basu gaskata annobar sarke numfashi ba, shi yasa suke karya doka wajen daukar fasinja fiye da kima wanda hakan ba daidai bane.
Ministan ya kara jan hankalin gwamnoni wajen ganin sun sa ido sosai akan masu harkar sufuri don ganin ba a tufka da warwara a lokaci daya.
Lai ya jadaddawa masu motar haya da ta gida cewa mutum uku kadai gwamnati ta amince musu su dauka a mota, wato mutum daya a kujerar gaba, sai biyu a kujerar baya.