A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta ce zata sake tura kwararru jihar Kogi domin sake sabon zama da masu ruwa da tsaki na jihar, domin ganin an kawowa jihar dauki game da cutar sarke numfashi.
Ministan Lafiya na kasa Dakta Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da kwamitin kar ta kwana kan annobar, jiya a Abuja.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa an samu rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar ta kogi da wakilin dalike cututtuka ta kasa NCDC, inda Gwamnatin jihar ta kafa musu wasu sharuda kafin su fara gudanar da aikinsu.
Rashin jituwar tasu yasa Gwamnatin Kogi taki amincewa tare da bada hadin kai, wanda hakan yasa wakilan na hukumar dakile cututtuka ta kasa suka bar jihar ba tare da sun samu cikakken goyon baya ba.
Ehanire yace yana da kyau a sake tura kwamitin kwararru domin zama da gwamnan jihar tare da kwamitinsa don ganin an yaki cutar a jihar.
Ministan ya kara da cewa ma’aikatarsa zata yi hadin guiwa da gwamnatocin jihar domin ganin an yi aiki tare.
A wani cigaban Ministan ya bayyana cewa kwamitin da aka tura jihar Cross Rivers sun dawo da bayanan inda jihar take bukatar tallafi.
“Sun kafa Kwamiti kan cutar sarke numfashin, tare da bada tallafin takunkimin fuska ga al’ummar jihar”.
“Sa ido da binciken yadda masu cutar suka yi mu’amala da wasu yana cigaba wanzuwa, kuma ana cigaba da bude wuraren gwaji wanda hakan ya fara saukaka aikin musamman ga jihohi”.