A kalla mutane 312 ne kasar Indiya ta kwashe daga Najeriya wanda dokar kulle ta ritsa da su sakamakon bullar annobar sarke numfashi tun a watan Maris.
Rahotanni sun bayyana cewa an kwaso mutanen ne daga filin tashi da saukar jirage na Murtala Mohammed dake jihar Legas da kuma Fatakwal.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-yan-najeriya-268-sun-iso-abuja-daga-kasar-china/
Babban kwamishinan kasar Indiya dake Abuja ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa jirgin Air peace shi ne jirgin da zai kwaso ‘yan kasar tasa domin su koma cikin iyalansu.
Kwamishinan ya kara da cewa jirgin zai kwaso ‘yan kasa Najeriya daga can kasar Indiya wanda suma dokar kulle ta ritsa dasu a yayin dawowarsa Najeriya.