A kalla Likitoci uku ne suka ne suka kamu da cutar Corona a jihar Nassarawa, hakan ya fito daga bakin shugaban kungiyar Likitoci reshen jihar Nassarawa Dakta Bulus Peter Umaru.
Shugaban ya kara da cewa Likitocin sun kamu da cutar ne a yayin da suke kula da masu dauke da cutar.
Shugaban, ya kara da cewa Likitocin yanzu haka suna cibiyar killace masu dauke da cutar ta gwamnatin tarayya.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-an-saki-shugaban-kungiyar-can-reshen-jihar-nassarawa/
Dakta Bulus, yace ya kamata likitoci suke daukar dukkanin matakan da aka bayar wajen ganin an dakile cutar, kuma suke amfani da rigunan kariya.
Shugaban ya sake kira ga gwamnatin jihar Nassarawa, akan ta bada umarnin biyan ‘ya’yan kungiyarsu ragowar kudadensu da suke bi.