Biyo bayan jawabin shugaban tawagar Shugaban kasa kan annobar COVID19 Aliyu Sani na cewa shugaba Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya Jawabi game da cutar COVID19 a yau Litinin, sai dai Fadar shugaban kasar ta yi mi’ara-koma baya, inda ta sanar da cewa shugaba Buharin ba zai yi wani jawabi a yau ba.
Mai magana da yawun shugaban kasa Mr. Femi Adesina shi ne ya bayyana hakan a Shafinsa na twitter.

Sanarawa tace wannan ba komai ba face yada labaran karya ne wanda ake yi a kafafun sada zumunta. Tun jiya ne dai aka dinga rade-radin cewa shugaba Buhari zai yi wa ‘yan kasar jawabi game da annonar Corona Virus.
Daga: Abubakar Muhammad Usman