Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa zata iya karawa ‘yan kasuwa rana daya daga cikin ranakun da zasu ke fitowa, matukar sun bi dokar da gwamnati ta gindaya musu.
Tun farko dama ‘yan kasuwar sun bukaci gwamnati da ta kara musu kwana daya daga cikin ranakun da zasu ke fita, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace matukar sun bawa gwamnatin hadin kai to tabbas za a cika musu bukatarsu.
Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin da yake jagorantar tawagar masu feshin magani a kasuwar sabon gari domin dakile cutar sarke numfashi da ma wasu cututtukan.
https://dimokuradiyya.com.ng/dokar-kulle-yadda-kasuwar-sabon-gari-da-wasu-kasuwanni-suka-yi-cikar-tsinke-a-karon-farko-da-aka-bude-kasuwanni-a-kano/
“Bamu da wani fata face mu ga bayan wannan cuta ta Corona, dan haka muna bukatar hadin kai daga jama’a don cimma wannam nasara”. Cewar Ganduje.
Gwamnan ya kara bawa mutanen jihar hakuri bisa zaman gida da ake fama da shi, inda yace hakan yana da matukar amfani wajen ganin an dakile cutar da ma wasu sauran cututtukan.