A wasan da kasar Portugal ta buga a daren jiya Litinin, fitaccen dan wasan kwallon kafarnan, wato Cristiano Ronaldo na kasar Portugal kuma dan wasan kungiyar Juventus ya zura kwallo ta 700 a tarihin kwallon kafarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu Ronaldo ya ci kwallaye 5 ga kungiyarsa ta farko wato Sporting CP guda 5, sannan ya zura kwallo 118 a lokacin da yake Manchester United, sannan ya zura kwallo 450 a lokacin da yake Real Madrid, da kuma kwallo 32 a kungiyarsa ta Juventus. Sai kuma ya ci wa kasarsa kwallo 95 wanda wannan ya kama kwallaye 700.
Duk da dai kasar ta Portugal ta yi rashin sa’ar nasara akan kasar Ukraine, inda Ukraine din ta ci su 2 da 1, amma Ronaldo ya zura kwallo 1 ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida.