An fitar da Canada daga gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar na shekarar 2022, bayan da ta sha kashi a hannun Croatia da ci 4-1 a yammacin ranar Lahadi. Kamar yadda Leadership ta ruwaito
Alphonso Davies ne ya fara zurawa Canada kwallo bayan dakika 68 kacal da fara wasan amma Andrej Kramaric ya zura kwallo ta biyu a wasan da ta taimakawa Croatia ta koma ta daya a rukunin F kafin wasansu na karshe.
KARANTA WANNAN LABARIN : Manchester United Na Fatan Kawo Dan Wasan Gaban Chelsea A Watan Janairu
Kramaric ya kara da wani bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 70, kuma dan wasan tsakiya, Lovro Mager, ya zura kwallo ta hudu a karawar da Croatia wanda ya kai ga fidda Canada daga wasan.
Sakamakon ya nuna cewa Canada ta ci gaba da zama ba tare da maki ba a rukunin F bayan da ta sha kashi a wasanni biyu na farko.
Belgium tana da maki uku yayin da Croatia da Morocco ke da maki hudu kowaccen su.
A wani labari kuma, FG Ta Tsawaita Ranar Fara Aikin Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna
Gwamnatin tarayya ta bakin ma’aikatar sufuri ta sanar da tsawaita wa’adin aikin layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.
Ministan Sufuri Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna ranar Lahadi a wani rangadin da ya kai don duba yanayin shirye-shiryen layin dogo na Abuja zuwa Kaduna kafin a fara aiki