Rundunar Sojin 13 Brigade dake karkashin Shirin yaki na Operation Akpakwu sun chafke wani matashi mai shekara 24 mai suna Kingsley Offiong bisa zargin sace wani matashi dan kimanin shekara 18 inda ya bukaci yan uwan shi da su biya kudin fansa.
Da yake gabatar da wanda ake zargin ga yan jarida, Kwamnadan rundunar ta 13 Brigade, birgediya Janar Abdullahi Muhammad ya ce an chafke shi ne a yankin Umo Urok kusa da gidan gyaran tarbiya dake karamar hukumar Kalaba ta Kudu.
Da yake wakiltar Kwamndan, Manjo Stanley Ikpeme ya ce matashin ya yaudare shi ne ta yanar gizo tun daga Karamar hukumar Ikom mai nisan kilomita 250 daga babban birnin jihar Calabar.
Tuni nkuma wanda ake zargin ya masa tuhumar da ake mishi inda ake jiran hukunci kotu bayan kammala gudanar da bincike.