Cristiano Ronaldo ya shirya tsaf don rage albashinsa domin ya tilastawa barin Manchester United.
A cewar UK Independent, Ronaldo zai amince a rage masa albashin da yake amsa na fam 500,000 a duk mako domin ya koma sabon kungiya.
An fahimci inda ya fi so shine Chelsea ko kuam Bayern Munich.
Dan wasan mai shekaru 37 yana da sha’awar taka leda a gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa kuma a shirye yake ya sadaukar da kansa don tabbatar da hakan.
Chelsea na bukatar mai cin kwallaye bayan Romelu Lukaku ya koma Inter Milan a matsayin aro na shekara daya.
ahalin yanzu kuma, Robert Lewandowski kuma yana kokarin tilastawa barin Bayern Munich zuwa Barcelona
A wani labarin kuma na daban
Kashi na 3 na horan mako guda ga ma’aikatan Kano da aka tura zuwa fannin ilimi ya fara aiki a shiyyoyin sanatoci 3 na jihar.
Da take kaddamar da shirin horaswar a shiyyar Kano ta tsakiya da kuma Kano ta Kudu, babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi, Hajiya Lauratu Ado Diso ta bayyana cewa horon zai kasance wani kwas ne na farfado da ma’aikatan da aka tura wadanda suka dade suna aiki a MDAs. ta yanda za su kai yadda ya kamata a fannin ilimi.
Wannan na kunshe a sanarwar da Jami’in yada labarai a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Aliyu Yusuf ya fitar, kuma aka rabawa manema labarai.
Sanarwar Ta ce ilimin da mahalarta taron suka samu wanda ya fi dacewa a fannin ilimi shi ya sa gwamnatin jihar ta tura su domin su ba da gudummawarsu wajen bunkasa ilimi.
A yayin da ta bukaci da su mayar da martani ga gwamnati ta hanyar koyan sabbin dabarun koyarwa, ta kuma karfafa musu gwiwa da su ci gaba da gudanar da ayyukansu da tsoron Allah.
A jawabansu daban daban a wajen taron, Shugaban Hukumar SUBEB, Dokta Danlami Hayyo da takwaransa na Hukumar Kula da Makarantun Alkur’ani da Islamiyya, Gwani Yahuza Gwani Danzarga, sun yi kira ga mahalarta taron da su tabbatar sun shiga wannan horon.
Sun yi nuni da cewa gwamnatin jiha ta kashe makudan kudade domin horaswar, don haka akwai bukatar mahalarta taron su kasance masu aiki da kuma amfani da abubuwan da ya kamata su koya a cikin shirin horon na tsawon mako guda.
Shima da yake nasa jawabin, Babban Sakataren KSSSMB, Dokta Bello Shehu ya yi kira ga mahalarta taron da su mai da hankali ta yadda za su amfana tare da inganta ayyukansu, yana mai jaddada cewa a lokacin da ya dace su ba da horon mataki-mataki ga sauran malamai.
A shiyyar Kano ta Arewa, Sakataren Zartaswa na STSB, Malam Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana shirin a matsayin kyakkyawan shiri na wannan gwamnati, musamman a kokarinta na bunkasa fannin ilimi na jiha.
Dokta Yakubu Ibrahim Wunti wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar Bayero Kano reshen kungiyar kula da harkokin ilimi ta Najeriya (NAEP), wadanda suka gudanar da horon, ya tabbatar wa mahalarta taron cewa horon zai kasance mai mu’amala da juna, don haka akwai bukatar hada kai da masu gudanarwa.
Sanarwar ta rawaito ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa hadin gwiwa da hukumar NAEP wajen horar da ma’aikatan da aka tura.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, shirin horaswar da aka yi wa lakabi da “Tsarin Koyarwa na Morden” yana da mahalarta 1,200 daga hukumomin da suka hada da KSSSMB, STSB, QISMB, KSSSMB, Hukumar Ilimi da manyan makarantu a karkashin ma’aikatar ilimi mai zurfi.