By Abbas Yakubu Yaura
Kabilar Irigwe ta Jihar Filato a ranar Litinin din data gabata ta yi Allah-wadai da kisan mutane 10 tare da lalata dukiyoyi a yankin Ta’agbe dake karamar hukum Bassa da wasu da ake zargin Fulani ne suka yi.
A karkashin inuwar kungiyar Irigwe ta CIPPND sun bayyana sabbin kashe-kashen a matsayin abin zargi da tsokana.
Kungiyar ta CIPPND a cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Dakta James Chohu, ya fitar, ta bukaci masu ruwa da tsaki na Irigwe akan bukatar gaggawar ta murya daya domin yin Allah wadai da wannan danyen aiki.
Chohu yace, “Muna yin Allah wadai da kisan da aka yi wa mutane 10 tare da lalata dukiyoyi a kauyen Ta’agbe dake karamar hukumar Bassa ta Jihar Filato, a makon jiya, muna kuma bayyana hakan da cewa ba wai kawai na dabbanci ba ne, a’a, da gangan ne, na tayar da hankali. kuma abin zargi.”
Sannan ya bayyana cewa binciken da kungiyar ta gudanar ya nuna cewa dakarun OPSH sun isa garin ne bayan mintuna 15 da maharan suka afkawa kauyen.