- Wata mata da tayi ciko a mazaunanta ta kuma shiga yin rawa, cikon ya faɗo.
- Matar tana rawa amma cikon ya goce daga ainihin inda ya kamata kafin ya sulluɓo ƙasa
- Bidiyan yaja hankalin makallata da dama.
Matar da ake magana a kai ta kasance a wajen wani biki, sanye da wata gajeriyar riga, da farin siket a jikinta.
Tana rawar waltz tare da wani saurayinta a filin rawa inda wasu ma’aurata suma suke girgiza mazaunansu yayin da gungun ‘yan kallo suka tsaye suna ta kallo.
Ɓangaren mazaunan matar ya kasance ya ɗaga sama ya kuma bar wajen da ya kamata tsaya sakamakon rawar da take yasa shi kaucewa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ya Rasu Bayan Da Aka Cire Masa Kodarsa Domin Sawa Mahaifiyarsa.
Bidiyan dai ya janyo da yawa daga waɗanda ke gurin mayar da hankalinsu kan matar domin ganewa idanunsu wannan abin kunyar da matar tayi.
Wata Wada Ta Yi Rawar Kece Raini A Tsakiyar Kasuwa
A WANI LABARIN KUMA:Wata kyakkyawar wada ta yi rawa cikin ladabi a cikin kasuwa kuma ta nishaɗantar da dimbin jama’a da suka taru suna kallonta.
@mhizbrief ne ya wallafa wannan bidiyon rawan rawar a shafinsa na TikTok.
A cikin bidiyon, jama’a da dama sun taru don kallon yadda matar ta fara rawa a tsakiyar titin da ke kasuwa.
Da yawa daga cikin ‘yan kasuwar sun bar abin da suke yi, suka mayar da hankalinsu kan kyakkyawar wadar a yayin da take nishaɗantar da su da rawar ta.
Matar ta yi rawa ga wata waƙar ƙasar da ke jin kamar ganga mai magana. Bidiyon ya zama hoto ko bidiyo wanda ya zagaya yanar gizo bayan ta sanya shi akan TikTok.
Mutane da yawa da suka kalli bidiyon rawar wadan sun shiga sashin sharhi don yaba kyawun matar da bajintar ta.
Ga abinda wasu daga ciki suke cewa, kamar yadda majiyarmu ta jiyo mana.
@chimkamalu ya ce: “Waw Wanna shine ganina da kyakkyawar wada kuma tsaftatacciya. Tabbas tana da kyau.”
@skinminceur ya mayar da martani: “Tana da kyau sosai.”
@Oumalher Maman Ghaly ya ce: “Tana da kyau sosai.”
@beauty ta ce: “Tana da kyau da kyau kuma siffarta tana ba da sha’awa.”
@smoothie yayi sharhi: “Ɗana yace min Umma yarinyar nan fa tabbas ta iya rawa, ba ƙarya fa.”
@Arikeolami ya ce: “Tana da kyau sosai.”
@yanoga12 ya mayar da martani: “Tana da kirki.”