Darakta-Janar na Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Ifedayo Adetifa, ya ce mutane 18,577 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kyanda da kuma mutuwar mutane 190 a cikin mako na 35 a jihohi 36 da babban birnin tarayya.
Ya bayyana hakan ne a Abuja jiya yayin taron ministoci da sabbin bayanai kan cutar COVID-19 da ci gaba da aka samu a bangaren kiwon lafiya.
A yayin taron ya samu wakilcin shugaban sashin bayar da amsa, sashen bayar da agajin gaggawa na kiwon lafiya a NCDC, Dokta Olaolu Aderinola, ya ce: “Akwai kananan hukumomi 40 da suka kamu da cutar. Muna ci gaba da tallafa wa jahohi game da barkewar cutar kyanda.”
KARANTA ANAN: An Samu Sabani Da Ministar Kudi Da Majalisar Dattawa Kan Kasafin Baɗi
Ya ce ana ci gaba da ganin tasirin COVID-19 a wasu yankuna da dama ciki har da karuwar barazanar cutar kyanda da yuwuwar karuwar barkewar cutar zazzabin shawara saboda jinkirta yakin neman rigakafin da aka shirya.
Daraktan shirin Lafiya na Port, karkashin Ma’aikatar Lafiya, Geoffrey Okatubo, ya ce an kama fasinjoji 422 dauke da katunan rigakafin COVID-19 na jabu a watan Yuli da Agusta.
Ya ce kashi 96 cikin 100 na fasinjojin da ke zuwa Najeriya an yi musu allurar COVID-19, amma yawancin fasinjojin da ke zuwa da kuma barin kasar sun sami katunan rigakafin COVID-19 na jabu.
Ya ce 176 daga cikin irin wadannan an same su ne a filin jirgin sama na Abuja a watan Yuli da kuma 246 a wasu filayen jiragen saman kasar a watan Agusta.
A wani labarin kuma: ‘Yan Sanda Sun Lalata Wata Haramtacciyar Matatar Mai A Benin
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musamman a kan harkokin man fetur ta lalata wata matatar mai ba bisa ka’ida ba a Benin.
An tattaro cewa tawagar sun fasa wurin ne a titin Agbor daura da Depot na PPMC a karkashin layin wutar da ke cikin birnin a bisa wani rahoto da suka samu kan yadda kungiyar take aikin tace man ba bisa ka’ida ba.