By Ishaq Dabai
Akalla mazauna jihar Jigawa mutum guda 720,000 ne aka yiwa aikin rigakafin cutar amai da gudawa wanda gwamnatin jihar Jigawa ta fara tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.
Da yake zantawa da da manema labarai, Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Kiwon Lafiya matakin Farko na Jihar Jigawa (JSPHCDA), Dakta Kabiru Ibrahim ya ce jihar ta karbi alluran rigakafin miliyan 1.4 daga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya don gudanar da aikin.
Ya kuma yi bayanin cewa za a yi allurar rigakafin ga mutane 720,000 da aka yi niyya a cikin kananan hukumomi uku da cutar tafi kamari, Birninkudu, Dutse da Hadejia.
Babban sakataren ya jaddada cewa za a yi allurar rigakafin a kan mutane daga shekara daya zuwa sama, yana mai cewa za a yi allurar cikin allurai biyu; makonni hudu bayan kashi na farko.
Kazalika “yawan mutanen da aka yi niyya sun kasance daga shekara daya zuwa duk shekarun da suka cancanci yin allurar yayin da wuraren da aka nufa sune manyan ƙananan hukumomin uku na Birninkudu, Dutse da Hadejia.”