By Ishaq Dabai
Kimanin sama da mutane 150 aka tabbatar sun mutu a cikin mutane da suka kamu da annobata amai da dudwa 5,677 tun bayan barkewar cutar ta a jihar Katsina a cikin wata daya.
Sakataren zartarwa na hukumar kulada da marasa lafiya matakin farko PHCDA, na jihar Katsina Dakta Shamsudeen Yahaya shine wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a yayin da yake tattaunawa da manajan lafiya na jihar, yace a kididdigar da sukayi su tattarata tane daga asibitoci da kuma wuraren kula da lafiya matakin farko na jihar.
Shamsudeen yace kididdigar mutane da suka kamu tana karuwane musamman ma mutane karkara wadanda basa son kai rahoton cutar asibiti.
Ya kara da cewa “hakan ce take faruwa a sauran yankunan kasar nan, har yanzu a kwai cutar a mai da gudawa a jihar Katsina, sannan mun sani cutar a mai da gudawa tafi kamari a lokacin damuna.
A ranar Talata 2 gawatan Satumba muna da masu cutar a mai da gudawa sama da mutum 5,677 a gaba daya kananan hukumomi 34 na jihar.
” A lokacin da mutane suke shiga cikin bola batare da la’akari da irin cututtukan da mutum zai dauka ba to dolene ma a yada cutar amai da gudawa”.
Kazalika yayi kira ga daukacin mutane da su zama masu tsaftar muhallansu da kula da lafiyar a bincin da sukeci, ta hakane kawai zasu inganta harkar samar da lafiyar muhallansu.