Gwamnatin Tarayya ta gargadi dukkanin asibitocin koyarwa dake fadin kasar nan da su tashi sun ankara sakamakon barazanar sake ballowar cutar Ebola da ake gani za ta iya fantsamowa kasar daga kasar Guinea Conakry.
Wannan na kunshe ne cikin wata takarda da Ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire ya fitar mai dauke da sa hannun Daraktan Tsare-tsaren Lafiya da Kididdiga Dakta Ngozi Azodoh ta Ma’aikatar a ranar 19 ga watan Afirelun da muke ciki.
Sanarwar ta ce ma’aikatar ita ba gaban kanta ta yi ba, ta yi wannan gargadi ne biyo bayan wani wasika da Ma’aikatar Harkokin wajen kasarnan ta aike mata da shi kan sake fantsamowar cutar wacce ta birkita kasar a baya.
Kazalika sanarwar ta ce baya ga nan, Kasar Laberiya ma ta gargade Najeriya da ta ankare wajen ganin an dakile sake bazuwar cutar a kasar da ma makwabta.
Idan za a iya tunawa a watan Fabrairun wannan shekara ne Hukumar dake kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta yi gargadi cewa Najeriya na kan ƙaya ne dangane da wannan muguwar cuta.
Yunkurin da Jaridar Leadership ta yo don jin ta bakin ma’aikatar Lafiyar ya ci tura sakamakon gaza daukar kiraye kirayen wayan da ma’aikatar ta yi.