Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana irin koma baya da muguwar cutar nan ta korona ta kawo wajen gina kasarnan.
Shugaban Kasar ya bayyana haka ne a daren jiya yayin da yake karɓar wata takardar girmamawa daga ƙasashen Bulgaria da China da Pakistan da Turkiya gami da kasar Ukraine.
Yayin da yake jawabi, Kakakinsa Femi Adesina ya bukaci hadin gwiwar kasashen duniya don ganin an kawo karshen cutar.
Kazalika shugaba Buhari ya mika kokon bararsa da a yi aiki Kafaɗa da Kafaɗa don ganin an dakile matsalolin tattalin arziki da sauran kalubale da ake fama da su.
Daga bisani Buhari ya ja hankalin yan kasa da su haɗa kai don dora ƙasar izuwa tudun na-tsira musamman a bangaren da ya shafi tsaro.