Franministan Birtaniya Boris Johnson lokacin da ya karbi rigakafin korona ta Astrazeneca a ranar 19 ga watan Maris din wannan shekara ta 2021.
Hukumar kula da harkokin kiwon lafiya a Burtaniya tace, cikin mutane 30 da suka fuskanci matsalar toshewar jini bayan sun karbi allurar rigakafin korona ta Oxford-AstraZeneca, bakwai sun mutu.
To sai dai Hukumar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da amincewa ayi musu allurar, bisa hujjar cewar, har yanzu fa’idojin maganin nada tasiri kan duk wani hadiri na annobar korona.
Yanzu haka kasashe da dama ciki har da na Turai a dari-dari da wannan rigakafi na kamfanin AstaraZeneca, ko da a ranar Jumma’a Netherlands ta bi sahun wasu kasashen Turai wajen dakatar da allurar rigakafin ta AstraZeneca ga mutanen da ke kasa da shekaru 60 saboda fargabar cutar daskarewar jini.
Wannan matakin ya biyo bayan sabbin kamuwa da cutar daskarewa jina har guda biyar a Netherlands wadanda suka shafi mata ‘yan shekaru 25 zuwa 65, daya daga cikinsu ta mutu.