NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 655 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Laraba.
Haka nan, mutum 11 sun sake mutuwa sakamakon cutar.
Bisa sabbin alkaluman hukumar, Jihar Legas ce kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 240 da aka tabbatar sun kamu da cutar.
Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 88 a jihar Ogun da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.
Mutum 56 kuma sun kamu da korona a Rivers, dake kudu maso gabashin Najeriya , sai Abuja babban birnin ƙasar da aka samu mutum 51 da Kaduna mai mutum 43 da suka kamu da cutar a wannan rana.
A jihar Kano an samu mutum 25, yayin da ƙarin mutum 21 suka kamu a Filato. .
Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi:
Taraba-19
Edo-17
Abia15
Delta-13
Nasarawa-11
Akwa Ibom-10
Kwara-10
Oyo-10
Kebbi-9
Borno-5
Bayelsa-4
Gombe-4
Ekiti-2
Osun-2
NCDC ta ƙara da cewa an sallami mutum 393 daga cibiyoyi daban-daban da ke jihohin Najeriya.
Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 153,842, an sallami 130,818 jumulla sannan mutum 1,885 sun mutu tun bayan da cutar ta ɓulla a Najeriya.