Cibiyar dake Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya (NCDC), ta ce ta sami karin mutuwar mutane takwas sakamakon rikicewar mummunan cutar korona ya zuwa ranar 2 ga Satumba, 2021.
NCDC ta tabbatar da hakan ne a shafinta na Intanet a ranar Juma’a, inda ta ce har wala yau an samu karin mutum 631 da suka kamu da cutar a tsakanin jihohi 19 ciki harda Birnin Tarayya Abuja.
Wannan adadin ya sanya wadanda suka kamu da cutar sun karu duba da adadin mutum 582 da suka kamu da cutar a ranar Laraba.
NCDC sun ce jihar Legas an samu mutum 172 da suka kamu da cutar, a yayin da jihar Oyo ke da mutum 93 sai Ribas da mutum 72.
Sauran sun hada da; Edo (63); Katsina (29); Abia (26); FCT (23); Kano (23); Bayelsa (20); Ogun (20); Ekiti (18); Anambra (16); Delta (16); Osun (14); Imo (11); Benue (6); Enugu (4); Jigawa (2); Niger (2) da Nasarawa (1).
NCDC ta ce ya zuwa yanzu tun bayan bullar cutar a Fabarairun 2020 mutum 193, 644 suka kamu da cutar a Nijeriya.
A inda aka sallami akalla 179, 249 daga asibiti bayan duba su da yi musu magani, cuta kuma ta kashe mutum 2,488.