• An Sami barkewar cutar kwalara a jihar Filato.
• Kwamishinan kiwon lafiya na jihar ne ya tabbatar da barkewar cutar ga majalissar zartarwar jihar.
• Cutar tayi sanadiyar mutuwar mutun goma sha hudu a fadin jihar.
Jihar Filato ta sami rahotan masu dauke da cutar kwalara 953, yayin da Mutum 14 suka mutu, inda kuma aka sallami mutun 910 masu dauke da cutar, Kuma 29 ke cigaba da amsan kula wa a wuraren kiwon lafiya daban-daban dake fadin jihar.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Dakta Nimkong Lar ne, ya bayyana wadannan adadin, lokacin da yake zantawa da majalissar zartarwar jihar a jiya Laraba, a fadar gwamnatin jihar dake garin Jos.
Inda ya ce, anfara samun mullar cutar ne a karamar hukumar Jos ta Arewa, daga bisani abun ya yadu zuwa wasu Kananan hukumomin goma sha uku dake jihar. Hakan yasa lamarin ya yi kamari da ya kamata a magance shi.
Lar ya kara da cewa, Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa wato NCDC, ta ruga da ta iso jihar, domin tallafa wa jihar ta Filato, wajan yaki da barkewar cutar a fadin jihar baki daya.
KARANTA WANNAN LABARIN: A daina yiwa Yan fim kallon yan iska
Kazalika ya ce, ” Karamar hukumar Jos ta Arewa ita ce, keda adadi mafi yawa na masu dauke da cutar Kwalara, inda ta ke da Mutum 484, Sai Karamar hukumar Jos ta Kudu, da Karamar hukumar Bassa, da suke bi mata a baya da adadin yawan mutun 307 da 57 ko wannan su,” inji shi.
Comments 1