Akalla mutane ashirin ne suka gamu da ajalinsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a kananan Hukumomi tara cikin ashirin na Jihar Bauchi.
Kwamishinan Harkokin Lafiya na jihar ta Bauchi Dakta Aliyu Maigoro shine ya sanar da haka a yayin wata zantawarsa da manema labarai a birnin na Bauchi.
Wakilin mu a Bauchi Bashir Khalid Furyam ya ruwaito mana cewa kananan hukumomin da al’amarin ya shafa sun hada da Bauchi da Darazo da Ganjuwa da Giade da Misau da Ningi da Shira da Toro gami da Ƙaramar Hukumar Warji.
Kwamishinan ya kuma ce tuni aka samar da cibiyar bada agajin gaggawa da kuma cibiyar Killace marasa lafiya a birnin Bauchi, da aniyar dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Bugu da kari Maigoro ya ce a yanzu haka ana nan ana shirye-shiryen samar da karin cibiyoyin kilace marasa lafiyar a manyan asibitocin kananan hukumomin sha da zummar takaita bazamar cutar ta Kwalara.
Daga bisani Kwamishinan ya yaba wa gwamnatin Jihar Bauchi da sauran Ƙungiyoyin bada tallafi bisa tashi tsaye wajen ganin an shawo kan cutar, tare da shawartar jama’a da su rungumi dabi’ar tsaftace jiki da muhalli a wani mataki na kare kai daga cutar.